30 Satumba 2020 - 11:29
Iran Ta Mika Sakon Ta'aziyya Ga Koweit Game Da Rasuwar Sarki Al-Sabah

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta aike wa Koweit da sakon ta’aziyya kan rasuwar sarkin kasar Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah.

ABNA24 : A wani sako da ya aike wa kasar, ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya ce, ya kadu da jin labarin rasuwar sarkin na Koweit, tare da yi masa fatan Allah ya jikansa.

Mista Zarif, ya danganta mirigayin da mutum na gari mai son ci gaba kasarsa dama yankin baki daya.

Haka kuma Iran, ta yi wa Koweit da al’ummarta fatan alhairi, da samun ci gaba da kwanciyar hankali karkashin sabuwar sarautar.

A jiya ne sarkin na Koweit, Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Sabah, ya rasu yana da shekaru 91 a duniya bayan fama da doguwar jinya a Amurka.

342/